TRENDING

Sanarwar da babban sakataren yaɗa labarai ga gwamnan Kano ya fitar a ranar Talata, na cewa ana zargin Dr. Tukur Ɗayyabu Minjibir ne da sayar da hatsin gwamnati ta hanyar da ba ta dace ba

 



Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin dakatar da shugaban kamfanin samar da kayan aikin gona na jihar (KASCO), bisa zargin shi da sayar da hatsi mallakar gwamnati.


Sanarwar da babban sakataren yaɗa labarai ga gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, na cewa a ranar Talata 12 ga watan Satumban 2023 ne, Gwamna Abba Kabir, ya bayar da wannan umarni.


Sanarwar ta ce ana zargin Dr. Tukur Ɗayyabu Minjibir, ne da sayar da hatsin gwamnati, ba ta hanyar da ta dace ba.


Gwamnatin jihar ta umarci Dr Tukur Ɗayyabu, ya miƙa ragamar gudanar da kamfanin ga jami'i mafi girman muƙami nan take, ya zuwa lokacin da za a ji sakamakon ƙarin bincike.


Farashin shinkafa zai tashin da bai taɓa ba cikin shekara 12 - MDD

Ko rushewar yarjejeniyar fitar da hatsi ta Ukraine za ta janyo ƙarancin abinci?

Abin da dokar ta-ɓaci kan samar da abinci ke nufi ga talakan Najeriya

Article share tools



View more share options

Share this post


Karanta karin bayanai 

kan wannan mashigin

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post